Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’Adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.

00:00
00:00

Resumen del episodio

A yau shirin zai leƙa Najeriya, inda aka samu saɓani ta fuskar alƙaluma a fannin ilimi, bayan fitar da sakamakon jarabawar ƙasa ta NECO na shekarar 2026, gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa jihar ce ta zo ta ɗaya a fadin ƙasar. Sai dai, wani bincike mai zurfi da jaridar Premium Times ta yi, ya musanta wannan iƙirari, inda ta ajiye jihar a matsayi na 31. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

Episodios

455-

Najeriya: saɓanin alƙaluma kan jihar da ɗalibanta ke kan gaba a cin jarabawar NECO

A yau shirin zai leƙa Najeriya, inda aka samu saɓani ta fuskar alƙaluma a fannin ilimi, bayan fitar da sakamakon jarabawar ƙasa ta NECO na shekarar 2026, gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa jihar ce ta zo ta ɗaya a fadin ƙasar. Sai dai, wani bincike mai zurfi da jaridar Premium Times ta yi, ya musanta wannan iƙirari, inda ta ajiye jihar a matsayi na 31. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

06 oct. 2026
454-

Jigawa ta gabatar da tsarin rage barace-baracen Almajirai a jihar

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan daɗaɗɗen batun nan na yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya matsalar da har kawo yanzu ta ƙi ci taki cinyewa. Wani Rahoton UNICEF ya bayyana jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a matsayin jihohin da ke da rinjayen yaren da basa zuwa Makaranta, inda a jumlace ƙasar ta yammacin Afrika ke da yara fiye da miliyan 18 da basa zuwa Makaranta, galibinsu a arewacin ƙasar. Tuni Jihar Jigawa ta ɗaura ɗamarar yaƙi da wannan matsala, inda ta gabatar da wani sabon tsarin mayar da ɗimbin yara makarantu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

29 sep. 2026
453-

Gwamnatin Kano na shirin tilasta koyar da ilimin Kwamfuta a makarantun Firamare da Sakandare

Shirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda majalisar dokoki jihar Kano ta bukaci a mayar da ilimin Kyamfuta dole a matakin makarantun Firamare da Sakandare. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

22 sep. 2026
452-

Gwamanatin Najeriya na shirin Horas da malamai sama da miliyan guda

A yau shirin ya mayar da hankali ne kan matakin gwamnatin Najeriya kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka da ke shirin horas da malaman makaranta sama da miliyan guda. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

15 sep. 2026
451-

Gudunmowa ko kuma illar da shafukan sada zumunta ke yiwa al'adun Bahaushe

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya duba irin yadda guguwar kafafen yada labarai da shafukan Internet ke barazana ga al'adun Hausawa da salon rayuwarsu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

01 sep. 2026