Resumen del episodio
Yau shirin zai mayar da hankali kan sabon rahoton Babban Bankin Nigeria, wanda ya fito da sabbin alkaluman ci gaban da aka samu a fannin damar iya sayen kayayyaki a kasuwanni a tsakanin al’ummar kasar da ya karu da maki 53 a watan Satumba daga maki 52.7 daga watan Agustan da ya gabata. Madallah! Lallai za’a yi cewa, tattalin arzikin Najeriya na farfadowa bisa alƙaluma, amma ga talakan ƙasar, har yanzu babu wani alamun sauƙi. A kasuwanni, farashin kayan abinci da sauran kayayyaki na ci gaba da kasancewa babban ƙalubale, yayin da ’yan kasuwa ke kokawa da tsadar sufuri da wutar lantarki..
Yau shirin zai mayar da hankali kan sabon rahoton Babban Bankin Nigeria, wanda ya fito da sabbin alkaluman ci gaban da aka samu a fannin damar iya sayen kayayyaki a kasuwanni a tsakanin al’ummar kasar da ya karu da maki 53 a watan Satumba daga maki 52.7 daga watan Agustan da ya gabata. Madallah! Lallai za’a yi cewa, tattalin arzikin Najeriya na farfadowa bisa alƙaluma, amma ga talakan ƙasar, har yanzu babu wani alamun sauƙi. A kasuwanni, farashin kayan abinci da sauran kayayyaki na ci gaba da kasancewa babban ƙalubale, yayin da ’yan kasuwa ke kokawa da tsadar sufuri da wutar lantarki..
Episodios
Rahoton CBN ya ce ƙarfin sayayyar ƴan Najeriya ya ƙaru a watan Satumba
EscuchadoYau shirin zai mayar da hankali kan sabon rahoton Babban Bankin Nigeria, wanda ya fito da sabbin alkaluman ci gaban da aka samu a fannin damar iya sayen kayayyaki a kasuwanni a tsakanin al’ummar kasar da ya karu da maki 53 a watan Satumba daga maki 52.7 daga watan Agustan da ya gabata. Madallah! Lallai za’a yi cewa, tattalin arzikin Najeriya na farfadowa bisa alƙaluma, amma ga talakan ƙasar, har yanzu babu wani alamun sauƙi. A kasuwanni, farashin kayan abinci da sauran kayayyaki na ci gaba da kasancewa babban ƙalubale, yayin da ’yan kasuwa ke kokawa da tsadar sufuri da wutar lantarki..
Dalilin da ya sanya aka fara haramta sana'ar jari bola a wasu sassan Najeriya
EscuchadoSana’ar tattara wa da sayar da tsofaffin ƙarafa da sauran tarkace wadda aka fi sani da ‘Bola Jari’ na daga cikin sana’o’i da dubban mutane masamman matasa ke dogaro da su a Najeriya. Amma a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sana’ar ta fuskanci babban ƙalubale, musamman saboda zargin cewa wasu masu tattara ƙarafa na amfani da ita wajen sayar da kayayyakin da aka sace daga tituna, gadoji, layin dogo da sauran muhimman abubuwan more rayuwa. Wannan ne ya sa wasu gwamnatocin jihohi suka ɗauki matakin dakatarwa ko haramta sana’ar baki ɗaya. Yanzu haka Ƙungiyar masu sana’ar ta jari bola ta yi barazanar tsunduma yajin aikin gargaɗi, ta hanyar dakatar da lodi ko sayar wa kamfanoni baraguzai da suke tattarawa. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Matatar matatar Ɗangote ta ƙaddamar da sayar da hannayen jarinta a hukumance
EscuchadoShirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan ƙaddamar da shiga matatar Ɗangote kasuwannin hannayen jarin Najeriya, a wani biki da aka gudanar a babban shelkwatan kasuwannin hannayen jarin Najeriya da ke Marina a birnin Legas, inda shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko da kansa ya kaɗa ƙararrawar buɗe shigar matatar a hukumance. Matatar ta sanya hannun jari biliyan 4 da miliyan 100 kasuwa, kan Naira 525 ga kowane guda, inda take fatan tara kusan Naira tiriliyan 2 da biliyan 150. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..............
Tasirin da saida hannun jarin matatar man Dangote ke da shi ga al'umma
EscuchadoShirin kasuwa akai miki dole na wannan lokacin, ya maida hankali ne kan yadda matatar Dangote ta shirya buɗe ƙofifinta ga al’umma domin su mallaki wani kaso a matatar mafi girma a Afirka, bayan da a karon farko ta sanar da shiga kasuwar hannayen jari. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........
Sharhi kan kalaman Alhaji Atiku na maido da tallafin mai a Najeriya
EscuchadoShirin ‘kasuwa akai miki dole’ a wannan mako tattauna ne kan wasu batutuwa da suka taso masu nasaba da siyasa da tattalin arziƙi a Najeriya, Inda muhawara ta kaure kan batun tallafin man fetur, bayan da ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar adawa ta ADC Alhaji Atiku Abubakar ya yi alƙawarini maido da tallafin man idan aka zaɓe shi a 2027, to amma nan da nan gwamnatin Najeriyar ta mayar da martani. Kalaman Atiku, sun tayar da kura tare da ƙara zafafa lamura a fannin siyasa da tattalin arzikin ƙasar, inda a ƙarshe, shugaba Bola Ahmed Tinubu, da kansa, ya fito ya soki lamarin. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmad Abba...............